Kimanin mutum dubu 9 da 179 ne suke karbar kulawa daga Cibiyoyin Kula da Masu Cutar mai karya garkuwar Jiki HIV a Jihar Jigawa

0 73

Kimanin mutane dubu 9 da 179 ne suke karbar kulawa daga Cibiyoyin Kula da Masu Cutar mai karya garkuwar Jiki HIV a Jihar Jigawa.

Shugaban Shirin Kula da Masu Cutar HIV na Jihar Jigawa Dr Adamu Shehu Bilyaminu, shine ya tabbatar da hakan ga manema labarai a lokacin da ake bikin ranar Cutar HIV ta Duniya.

Shugaban wanda Jami’in Fasaha na Shirin Dr Zaharadden Abdullahi, ya wakilta, ya ce Jihar Jigawa tana daga cikin Jihohin da suke da karancin masu kamuwa da cutar ta kaso 0.3 cikin 100.

A cewarsa, daga cikin mutane dubu 11,471 da suke dauke da cutar HIV a jihar nan, mutane dubu 9,179 ne kadai suke karbar Magani.

Dr Zaharaddeen Abdullahi, ya ce Gwamnatin Jihar Jigawa tana aiki tare da kungiyoyin na Duniya domin bibiyar sauran mutanen da suke dauke da cutar kuma basa shan magani domin dawo da su kan hanya.

Haka kuma ya ce tsangwama na daya daga cikin dalilan da suke sanya mutane daina zuwa karbar magani.

Kazalika, ya ce dokar da Majalisar dokokin Jihar Jigawa tayi na yin gwajin cutar kafin aure na daga cikin hanyoyin dakile yaduwar cutar a jihar nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: