Kimanin Yara Mata da Almajirai dubu 36,800 ne aka saka su Makaranta ta cikin shirin BESDA a Jihar Jigawa, wanda Bankin Duniya da Gwamnatin tarayya suka kirkira.
Shugaban Shirin na Jiha Malam Magaji Idris Gumel, shine ya bayyana hakan a lokacin da yake tattaunawa da Manema Labarai a Dutse.
A cewarsa, an fara gudanar shirin ne a Kananan Hukumomi 15 na Jihar Jigawa domin kara yawan Yaran da basa zuwa Makaranta ya karu.
Malam Magaji Idris Gumel, ya ce sauran kananan hukumomin suma suna kan hanya domin ganin cewa ana aiwatar da shirin a sauran yankunan Jihar Jigawa.
Kazalika, ya ce an dauki Ma’aikata 920 domin su rika kulawa da gudanar da aiki domin ganin cewa shirin ya kai ga Nasara.