
A wani rahoto da rundunar ‘Yan Sandan Jihar Jigawa ta wallafa wa mane ma labarai a ranar Juma’a 4 ga watan Yuli, 2025; Rundunar ta ce tana gudanar da bincike kan wani mummunan lamari na kisan gilla da ya faru a ranar 1 ga Yuli, 2025 da misalin karfe 3:30 na rana a kauyen Galadanchi, karamar hukumar Dutse, inda wani tsoho dan shekara 70 ake zargin ya kashe ‘yar’uwarsa saboda rikici kan rabon ƙasar gado.
Binciken farko ya nuna cewa wanda ake zargi, Adamu Yakubu, ɗan shekara 70 da ke zaune a Galadanchi, ya buge ‘yar’uwarsa Hannatu Hashimu, mace mai shekaru 45, a lokacin wata muhawara mai zafi da suka yi game da rabon gadon ƙasarsu.
Rigimar da ta fara da gardama ta ƙara tsananta har ta kai ga musayar yawu a tsakaninsu, inda ake zargin Adamu ya ɗauki sanda ya bugi Hannatu.
Marigayiyar ta bar gidan da kuka, amma bayan ta isa gidanta ta yanke jiki ta faɗi. An garzaya da ita zuwa Asibitin Gwamnati na Dutse, inda likita ya tabbatar da mutuwarta.
Rundunar ‘yan sanda ta kama wanda ake zargin, kuma yana hannunsu domin gudanar da bincike. An kuma kwace sandan da aka yi amfani da shi a matsayin sheda.
Rundunar ‘yan sandan ta yi Allah-wadai da wannan mummunan lamari, kuma ta jaddada cewa ba za ta bari a tauye hakkin marigayiyar ba. Haka kuma, ta shawarci jama’a da su dinga warware rikice-rikicen da suka shafi su, musamman ‘yan uwa na jinni, da na ƙasa ta hanyayoyin da suka dace bisa doka.
Bayan kammala bincike, za a gurfanar da wanda ake zargi a gaban kotu. Haka kuma Rundunar ‘yan sanda ta Jihar Jigawa na mika ta’aziyyarta ga iyalan mamaciyar, tare da tabbatar wa da al’umma cewa za ta adalci.