Kiswatul Ka’abah a ƙasar Saudiyya ta bada lambar yabo da girmamawa ga Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jigawa
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta sake samun lambar girmamawa ta Kiswatul Ka’abah a ƙasar Saudiyya, lambar da ke nuna girmamawa da yabo ga ƙoƙarin da hukumar ke yi wajen gudanar da aikin Hajji cikin tsari da nagarta.
Wannan lambar yabo ta fito daga Dalil Al-Alim, wata hukuma da ke kula da ayyukan Hajji da alhazai a Saudiyya, wadda ta zaɓi Jihar Jigawa bisa la’akari da yadda ta cika ka’idoji da ƙa’idojin gudanar da aikin Hajji cikin nasara da ƙwarewa, idan aka kwatanta da sauran jihohin Najeriya.
A cewar hukumar, Jigawa ta cancanci wannan lamba ne saboda:
Babu ɗaya daga cikin alhazan jihar da aka ƙi ba shi visa,
An sauke alhazanta kusa da Masallacin Harami,
An tabbatar da cewa alhazan sun samu abinci sau uku a rana,
Da kuma wasu muhimman abubuwa na jin daɗi da sauƙaƙe musu aikin ibada.
Da yake tsokaci kan wannan girmamawa, Daraktan Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa, Alhaji Ahmed Umar Labbo, ya bayyana cewa gaskiya da adalci su ne tushen nasarar da suka samu.
Ya kuma yaba wa ma’aikatan hukumar saboda jajircewa da ƙoƙarin da suka nuna wajen tabbatar da nasarar aikin Hajjin bana.
Wannan ci gaba ya ƙara ɗaga darajar Jihar Jigawa a idon duniya, musamman ma a tsakanin jihohin da ke gudanar da aikin Hajji daga Najeriya.