Klub ɗin Al Hilal na Saudiya ta ware Yuro miliyan 300 don ɗauko Raphinha daga Barcelona

0 184

Klub din Saudiya ya ware zunzutun ƙudi har Yuro miliyan 300 domin ɗauko ɗan wasan Barcelona ɗan ƙasar Brazil Raphael Dias Belloli da aka fi sani da Raphinha.
Bayan suɓucewar manyan ƴan wasa irinsu Mohamed Salah wanda ya sabunta kwantiraginsa da Liverpool da Vinicius Jr. wanda shi ma zai kulla sabuwar yarjejeniya da Real Madrid, yanzu haka ƙungiyoyin Saudiyya sun karkata akalarsu zuwa ɗaya daga cikin fitattun taurarin FC Barcelona.

Rahotanni na cewa hankalin ƙlub ɗin Al Hilal na Saudiya ya karkata ga kyaftin ɗin Barcelona Raphinha wanda yanzu haka ke kan ganiyarsa a La Ligar Spain.

Al Hilal ta shirya bai wa Raphinha kwangilar shekaru hudu wadda za ta rika biyan sa Yuro miliyan 50 duk kakar wasa wato miliyan 200 har zuwa shekarar 2029.

Al Hilal ta kuma fara tuntuɓar FC Barcelona, domin ta sallama masa ɗan wasan da Yuro miliyan 100.

Leave a Reply