Korafe-korafen fyade 178 aka samu a jihar Jigawaa cewar Cibiyar Lura da Yaran da Kuma Matan da aka yiwa Fyade

0 104

Cibiyar Lura da Yaran da Kuma Matan da aka yiwa Fyade ta Jihar Jigawa ta ce kimanin korafe-korafen fyade 178 ta samu daga watan Janeru zuwa Agustan wannan shekarar fiye da 137 wanda aka samu a shekarar da ta gabata.

Mataimakin Gwamnan Jiha, Malam Umar Namadi, shine ya bayyana hakan a wani taron kwana 1 da aka shirya domin inganta fannin Lafiya tare da hadin gwiwar masu ruwa da tsaki, wanda aka shirya a Cibiyar Horas da Ma’aikata ta Manpower dake Dutse.

A cewarsa, gwamnatin jihar Jigawa ta damu da yadda ake samun karuwar korafe-korafen fyade a kullum.

Haka kuma ya bayyana cewa domin magance matsalar gwamnatin Jihar Jigawa ta sanya dokar daurin rai da rai ko kuma kisa ga wanda aka kama da laifin.

Mataimakin Gwamnan ya ce wasu daga cikin matsalolin da Gwamnatin jiha take samu shine yadda Iyaye suke boye abinda ya faru ta hanyar kin fadawa Jami’an tsaro.

Ya ce kuma gwamnatin jiha zata kara kudaden da ta ware wannan matsalar domin tunkarar ta tare da tallafawa wadanda lamarin ya shafa.

Kazalika, ya ce gwamnatin jiha zata kara kirkirar Cibiyoyin kula da wadanda aka ciwa zarafi a jihar nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: