kotu ta bayar da umarni a ƙwace dala miliyan 1.4 daga hannun Godwin Emefiele

0 133

Wata babbar kotun tarayya da ke zama a Legas ta bayar da umarnin a ƙwace dala miliyan 1.4 daga hannun tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele.

Mai shari’a Ayokunle Faji ya yanke hukuncin cewa, an bai wa gwamnatin tarayya kuɗaden ne, biyo bayan buƙatar da hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Najeriya, EFCC ta shigar.

A baya dai hukumar ta EFCC ta samu umarnin wucin gadi na karɓe kuɗaden a ranar 29 ga watan Mayun 2014

A zaman kotun, lauyan EFCC, Misis Bilkisu Buhari-Bala ta bayyana cewa kuɗaden sun samu ne ta haramtattun ayyuka da Emefiele ya gudanar.

Umarnin ƙwace kuɗin na dala miliyan 1.4 ya zo ne kwanaki kadan bayan da kotun ta bayar da umarnin a ƙwace kadarorin da suka kai naira biliyan 12.18 daga hannun Emefiele.

Leave a Reply

%d bloggers like this: