Kotu ta bayyana ayyukan kungiyoyin ƴan bindiga da ƴan ta’adda a matsayin ayyukan ta’addanci

0 123

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayyana ayyukan kungiyoyin ‘yan Bindiga da ‘Yan Ta’adda a matsayin ayyukan ta’addanci.

Alkalin kotun Taiwo Taiwo, ya bayar da umarnin kan bukatar da gwamnatin tarayya ta shigar.

Daraktar shigar da kara na ma’aikatar shari’a ta tarayya Mohammed Abubakar, wanda ya shigar da karar, ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da matakin, wanda manufarsa ita ce haramta ayyukan ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda da sauran kungiyoyin ta’addanci a kasarnan.

Kuma a wasu bayanai da ya gabatar, gwamnatin tarayya ta ce bayanan tsaro, sun tabbatar da ‘yan bindiga na kisa da satar mutane da fyade da sauran miyagun ayyuka a arewa maso gabas da yankin arewa ta tsakiya da kuma sauran sassan kasarnan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: