Wata Kotun gwamnatin tarayya wanda take zamanta a birnin tarayya Abuja, ta hana hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa INEC dakatar da Rijistar zabe daga ranar 30 ga watan Yunin 2022.

Hukumar INEC ta sanya ranar 30 ga watan Yunin da muke ciki a matsayin ranar dakatar da Rijistar katin zabe, a kasa baki daya a wani yunkuri na cigaba da shirye-shiryen babban zaben shekarar 2023 mai zuwa.

Hukumar Yaki da Cin hanci da rashawa da kuma tabbatar da shugabanci Nagari wato SERAP da kuma wasu yan Najeriya su 185 ne suka shigar da karar hukumar INEC a gaban Kotun.

SERAP ta ce akwai bukatar hukumar INEC ta kara wa’adin cigaba da yin rijistar katin masu zaben, kamar yadda ta yiwa Jam’iyun siyasa a lokacin da suke kokarin yin zaben fidda gwani.

Haka kuma SERAP ta bukaci Kotun ta yiwa dokar kara wa’adin rufe Rijistar zaben fassara, kan ko hakan ya sabawa kundin tsarin mulkin kasa na 1999 wanda aka sake yiwa kwaskwarima, da kuma Dokar Zabe.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: