Kotu ta sa ranar yanke hukunci ga masu fasaƙaurin tururuwa

0 106

Wata kotu a Nairobi, babban birnin ƙasar Kenya ta sanya ranar bakwai ga watan Mayu, domin yanke hukunci ga wasu mutane huɗu da ake zargi da fasaƙaurin tururuwa don fitar da su daga Kenya.

Mutanen sun haɗa da ɗanƙasar Vietnam, Duh Hung, ɗanKenya, Dennis Ng’ang’a da kuma wasu ƴan Belgium biyu, Lornoy David da Seppe Lodewijckx.

Kotun ta yi taiƙaitaccen zama a ranar Laraba, kafin ɗage zamanta zuwa ranar yanke hukuncin.

Tuni dukkaninsu suka amince da tuhumar da ake yi musu.

Hukumomi sun ce biyu daga cikin mutanen sun shiga ƙasar ne a matsayin ƴan yawon buɗe idanu.

Masu bincike sun ce an ɓoye turuwar fiye da 5,000 masu rai, a wasu ƙananan robobi da kuma sirinji.

A cewar hukumar kula da namun daji ta ƙasar, (KWS), ana safarar nau’ukan turuwar ne zuwa kasuwannin nahiyar Turai da na Asiya.

Inda ake sayar da kowace turuwa uwa, a kan dala $130.

Ana ɗaukar hukuncin da za a yanke a matsayin mai matuƙar muhimmanci, kuma irinsa na farko da zai kafa tarihi a ƙasar.

Leave a Reply