
Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta buƙaci majalisar dattijai da ta dawo da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, wanda aka dakatar a watannin baya.
Mai shari’a Binta Nyako, wacce ta yanke hukuncin, ta bayyana tsawon lokacin dakatarwar a matsayin ta yi tsauri da tsayi sosai ba tare da wata kwakkwarar hujja ta doka ba.