Kotu ta yanke wa mai kamfanin crypton da ya durƙushe zama gidan yari a Amurka

0 58

Wata kotu a Amurka ta yanke wa Alex Mashinsky, mamallakin kamfanin cryptocurrency nan da ya druƙushe, Celsius zaman kurkuku na shekara 12.

Tun a watan Disamban da ya gabata ne ɗan kasuwar, wanda ɗan asalin Isra’ila ne mazauna Amurka ya musanta dukkan zarge-zarge guda biyu da ake masa.

Mai shigar da ƙara ya ce Mashinsky ya damfara masu zuba jari, inda ya zambace su da cewa akwai riba sosai a kamfaninsa.

Da kamfaninsa ɗin ya durƙushe a shekarar 2022, an ruwaito cewa sama da mutum dubu 100 ne kuɗaɗensu ya narke, inda suka yi asarar sama da kadarorin dala biliyan huɗu.

Leave a Reply