Kotu ta yankewa wani malamin makarantar firamare hukuncin daurin rai da rai bayan ta kamashi da lalata da yar firamare mai shekaru 5

0 128

Wata babbar kotu dake zamanta a karamar hukumar Kazaure a anan jihar Jigawa,ta yankewa wani malamin makarantar firamare mai suna Makasusi Sunusi, hukuncin daurin rai da rai, bayan ta kamashi da lalata wata yarinya yar firamare yar shekara 5.

Lauyan da ya shigar da karar, ya zargi Sunusi, da yaudarar yarinyar a ranar 4 ga watan Fabrairu inda yayi mata fyade.

Hakanne yasa suka gabatar da shi a gaban kotu, kuma lauyan ya gabatar da shaidu 5 da kuma rahoton asibiti wanda ya tabbatar da cewa wanda ake zargin ya aikata laifin.

Mai shariar Justice Hussaina Adamu Aliyu, bayan ta bibiyi zaman kotun na yau, ya tabbatar da cewa wanda ake zargin ya aikata laifin.

Hakanne yasa ya yanke masa hukuncin daurin rai da rai a gidan yari, kamar yanda sashi na 3 na kundin manyan laifuffuka na jihar Jigawa wanda akayiwa kwaskwarima a 2014 a tabbatar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: