Kotu ta yi fatali da karar da kungiyar dalibai ta kasa NANS ta shigar na tilastawa gwamnatin tarayya da ASUU janye yajin aikin da suke yi

0 52

Kotun ma’aikata ta kasa a jiya ta yi fatali da karar da kungiyar dalibai ta kasa NANS ta shigar na tilastawa gwamnatin tarayya da kungiyar malaman jami’o’i ASUU janye yajin aikin da suke yi.

Alkalin kotun, mai shari’a Polycarp Hamman a hukuncin da ya yanke, ya dakatar da ci gaba da shari’ar a kan lamarin bayan da mai kara Umar Lawal ya janye karar da ya shigar.

Umar Lawal ya shigar da kara ne a ranar 16 ga watan Satumba, da kansa da kuma a madadin kungiyar dalibai ta kasa kan ministan ilimi, da kungiyar malaman jami’o’i da kuma babban lauyan gwamnatin tarayya.

To sai dai a jiya ne batun da ake shirin saurara a kotun, Umar Lawal ya sanar da kotun cewa ya shigar da bukatar neman a dakatar da karar.

Ya kara da cewa ya yanke shawarar janye karar ne saboda kungiyar dalibai ta kasa ta na kalubalantar mukaminsa a matsayinsa na shugabanta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: