Kotun Ƙoli za ta yanke hukunci kan zaben gwamnonin jihohin Kogi da Bayelsa

0 121

Alƙalan Kotun Ƙolin Najeriya sun kammala sauraron bayanan kowane ɓangarori a game da gwamnonin jihohin Kogi da Bayelsa.

Da Muritala Ajaka na Jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) A Jihar Kogi ne da Timipre Sylva na Jam’iyyar Progressives Congress (APC) a Jihar Bayelsa suke ƙalubalantar sakamakon zaɓen wanda Hukumar INEC ta sanar a zaɓukan na 2023.

Amma a ranar Litinin, Kotun Ƙolin ta sanar da cewa za ta sanar da ranar da za ta bayyana hukuncinta a game da shari’o’in guda biyu.

Idan ba a manta ba, Ajaka ya ɗaukaka ƙarar hukuncin Kotun Sauraron Ƙararrakin Zaɓen ne yana ƙalubalantar nasarar Ahmed Usman Ododo na Jam’iyyar APC a matsayin Gwamnan Kogi.

Haka kuma bayan hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙarar, Ajaka ya yi zargin cewa akwai kura-kurai a hukuncin.

A hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙarar kotun ta tabbatar da hukuncin ƙaramar kotun, inda ta yi watsi da ɗaukaka ƙarar da Ajaka.

Sai dai jim kadan bayan hukuncin ne Ajaka ya fito ya bayyana cewa zai tafi Kotun Ƙoli, domin a cewarsa, yunƙurin ƙwato haƙƙinsa ba zai tsaya a Kotun Ɗaukaka Ƙara ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: