wani barawo zai shafe watanni 9 a gidan yari.

Wannan na zuwa ne bayan wata babbar kotun majistare da ke Birnin Kudu a jihar Jigawa ta yanke wa matashin mai suna Bashir Abdullahi mai shekaru 28 hukuncin daurin watanni tara a gidan yari bisa samunsa da laifin satar babur da darajar kudinsa ta kai kimanin naira dubu dari da ashirin.

An yanke wa Bashir Abdullahi hukuncin dauri ne biyo bayan tuhumar da ake masa na aikata laifuka biyu da suka hada da shiga gida babu izini da kuma sata, lamarin da ya sabawa wasu sassan kundin manyan laifuka na Penal code.

Wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar tsaro ta farin kaya civil defense reshen jihar Jigawa, Adamu Shehu ya fitar a yau, ta ce an yankewa wanda ake tuhuma hukuncin daurin watanni 6 a gidan yari da tarar naira dubu 10 bisa samunsa da laifin shiga gida babu izini sai zaman gidan yari na watanni 3 tare da tarar naira dubu 20 bisa laifin sata.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: