Kotun ma’aikata ta kasa ta dage sauraron karar gwamnatin tarayya ta shigar akan (ASUU)

0 75

Kotun ma’aikata ta kasa da ke Abuja, karkashin jagorancin mai shari’a P.I. Hamman a jiya ta dage sauraron karar da gwamnatin tarayya ta shigar akan kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) zuwa ranar 16 ga watan Satumba, biyo bayan bukatar da kungiyar kare hakkin zamantakewa da tattalin arziki SERAP ta gabatar.

Mai shari’a Hamman ya dage shari’ar ne bayan lauyan SERAP, Ebun-Olu Adegboruwa ya ce kungiyar SERAP a ranar 8 ga watan Satumba ta shigar da kara a gaban kotu inda ta bukaci kotu ta tilasta wa gwamnati ta mutunta yarjejeniyar da ta kulla a shekarar 2009 da malaman jami’o’in da suke yajin aiki.

Mai shari’a Hamman ya ce kotun bata kai ga sauraron karar bukatar kungiyar SERAP ba.

Ya ce za a mika lamarin ga wani alkali domin ya yanke hukunci da zarar hutun ma’aikatan bangaren shari’a ya kare.

Tun da farko, lauyan gwamnati, Tijjani Gazali, ya nuna adawa da bukatar hada kararraki biyu.

Lauyan kungiyar ASUU, Femi Falana, ya ce yana sane da kararrakin da ke gaban kotuna.

Leave a Reply

%d bloggers like this: