Kotun Musulunci da ke Kano za ta yanke hukuncin shari’ar Shafiu Abubakar Gadan wanda ake zargi da ƙona masallata
Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke Kano za ta yanke hukunci a yau litinin kan shari’ar Shafiu Abubakar Gadan, wanda ake zargi da ƙona masallata a karamar hukumar Gezawa yayin sallar asuba, lamarin da ya haifar da asarar rayuka masu yawa.
Wannan mummunan lamari da ya faru ranar 16 ga Mayu, 2024, inda ya kashe mutane 17 nan take, daga bisani adadin ya ƙaru zuwa 25 sakamakon raunukan da wasu suka samu.
Ana tuhumar Shafiu da laifuka guda uku ciki har da jikkata mutane da kuma kisan kai.
Ya amsa laifinsa a baya, lamarin da ya sa alkalin da ke jagorantar shari’ar, Khadi Dalhatu Huza’i Zakariya, ya umurci a ci gaba da tsare shi a gidan gyaran hali har zuwa ranar yanke hukunci.
Lauyan Gwamnatin Jihar Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Haruna Isah Dederi ne ke jagorantar gurfanar da wanda ake zargi.
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya kai ziyara wurin wadanda suka jikkata a Asibitin Kwararru na Murtala, inda ya yi Allah-wadai da harin kuma ya tabbatar wa iyalan mamatan cewa za a tabbatar da adalci. Ya kuma bayyana cewa rikicin iyalai ne ya haifar da lamarin, ba laifi ne da ya danganci ta’addanci ko rikicin siyasa ba.