Kuɗin da Najeriya ke kashewa wajen shigo da man fetur daga ƙasashen waje ya ragu da fiye da naira tiriliyan 2

0 141

Hukumar ƙididdiga ta kasa, NBS ta ce kuɗin da Najeriya ke kashewa wajen shigo da man fetur daga ƙasashen waje ya ragu da fiye da naira tiriliyan biyu.

Cikin wani sabon rahoto da hukumar ta fitar ta ce a shekarar da ta gabata daidai wannan lokaci, NAjeriya ta kashe naira tiriliyan 3.81 wajen shigar da man fetur ƙasar.

NBS ta ce an samu raguwar kashi 54 cikin 100 idan aka kwatantan da shekarar 2024.

Raguwar ta samu ne sakamakon ƙaruwar samar da man fetur a cikin gida, musamman daga matatar man Dangote,m, a cewar hukumar ta NBS.

Ƙarin samar da fetur daga matatar Dangote ya rage dogaro da fetur daga kasashen waje, wanda Najeriya ta daɗe tana yi.

Alƙaluman ƙididdigar shekara biyar da suka gabata sun nuna ƙaruwar shigo da man fetur har zuwa shekarar 2024.

A zangon farko na 2020, an shigar da fetur na naira biliyan 732 inda ya ƙaru zuwa naira tiriliyan 1.29 a 2021, sannan ya ninka zuwa naira tiriliyan 2.69 a 2022.

Rahoton ya kuma nuna cewa man fetur shi ne kayan da aka fi shigar da shi daga ƙasashen ECOWAS zuwa Najeriya a zangon farko na 2025, inda ya kai naira biliyan 89.18 – wanda ya kai kaso 44.51 cikin 100 na dukkanin kayayyakin da aka shigar da su daga yankin.

Leave a Reply