Kun kusa kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya – Shugaba Buhari

0 89

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci zaman majalisar tsaro ta kasa a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Zaman ya tattauna ne kan yanayin tsaro da ake ciki a kasarnan.

Zaman ya samu halartar mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo; sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha; Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Babagana Monguno.

Sauran wadanda suka halarci zaman sun hada da babban lauyan gwamnati kuma ministan shari’a, Abubakar Malami; Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola; Ministan Harkokin Waje, Geoffrey Onyema; takwaransa na harkokin ‘yan sanda, Mohammed Dingyadi da kuma ministan tsaro, Bashir Magashi.

Babban Hafsan Tsaro, Janar Lucky Irabor; Babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Farouk Yahaya; Babban Hafsan Sojin Ruwa, Vice Admiral Awwal Gambo; babban hafsan sojin sama, Air Marshal Isiaka Oladayo Amao; da Shugaban Hukumar Leken Asiri ta kasa, Manjo Janar Samuel Adebayo, su ma suna halartar taron.

Leave a Reply

%d bloggers like this: