

- Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC ta rufe kamfanonin ruwa guda 10 a jihar Ondo bisa rashin bin ka’idoji - July 4, 2022
- Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar AA, Hamza Al-Mustapha, ya ce jam’iyyarsa ba za ta yi hadin gwiwa da mutanen da basu damu da makomar al’umma ba - July 4, 2022
- Yadda wani mutum ya kona matarsa bayan ya gama dukanta a jihar Ogun - July 4, 2022
Kungiyar Dalibai ta Kasa NANS ta caccaki gwamnatin tarayya da Kungiyar Malaman Jami’o ta ASUU, bisa gazawar su wajen cimma matsaya wanda hakan ne ya tirsasawa Malaman shiga yajin aiki.
Shugaban Kungiyar na Kasa Asefon Sunday Adedayo, shine ya bayyana bacin ran kungiyar cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai, inda ya yi barazanar cewa Daliban zasu gudanar da zanga-zanga domin tirsasawa Malaman komawa aji.
Kungiyar ASUU a jiya ta tsindima yajin aiki na gargadi, biyo bayan gazawar gwamnati wajen cimma yarjejeniyar da aka kulla tsakanin su.
Shugaban ASUU Farfesa Emmanuel Osodeke, a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a Lagos, ya ce kungiyar bata son shiga yajin aiki, sai dai sun yanke fara yajin aikin ne saboda gazawar gwamnatin tarayya wajen cika Alkawarin da ya dauka.
Farfesa Emmanuel, ya ce tsarin biyan Albashi ga Malaman na bai daya IPPIS, wanda gwamnati ta bijiro da shi da kuma UTAS wanda Malaman suka suka bijiro dashi na daya daga cikin dalilan shiga yajin aikin.
Shugaban Kungiyar Daliban ta NANS ya dora Alhakin shiga yajin aikin Malaman Makarantar akan ASUU da gwamnatin tarayya.