Kungiyar Dattawan Arewa ta zargi gwamnatin Kano da yunkurin durkusar da sarautun gargajiya

0 228

Kungiyar Dattawan Arewa, ta zargi gwamnatin jihar Kano da yunkurin durkusar da sarautun gargajiya a kasar nan, tare da rage tasirin karfin sarakuna.

Wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai na kungiyar Dattawan Arewa, Abdul-Azeez Suleiman ya fitar, ta bayyana cewa yawaitar dorawa da saukewa na masarautun da ake yi a Kano wani yunkuri ne karara na durkusar da masarautar da kuma rage ikon sarakunan gargajiya.

Ya kara da cewa, ta hanyar samar da masarautu da dama, ana rage karfi da tasiri na sarakunan gargajiya ne, wanda hakan zai saukaka wa ‘yan siyasa damar sarrafa su yadda suke so.

Ya koka da cewa matakin ba wai yana barazana ga hadin kan tsarin gargajiya ba ne, har ma yana lalata al’adu da dabi’u da suka dade a shekaru aru-aru da suka kasance ginshikin al’ummar Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: