Kungiyar dattawan jihar Zamfara ta koka kan yadda hukumomi a jihar suka saki ‘yan fashin daji da masu taimaka musu, ba bisa ka’ida ba.

Kungiyar ta bukaci jami’an tsaro da su dakatar da wannan aika-aikar, inda ta bayyana hakan a matsayin daya daga cikin abubuwan da suka haddasa tabarbarewar tsaro a jihar.

Ta bayyana hakan ne a yayin taron ta a Gusau, babban birnin jihar, inda ta kuma koka kan halin da ‘yan fashin dajin suka jefe kananan yara marayu.

Wani tsohon Sanata, Saidu Dansadau, ya zanta da manema labarai bayan kammala taron.

Ya ce kungiyar ta kuma bayar da shawarar sake farfado da kungiyoyin al’umma domin samar da kudade don kafa makarantun firamare da sakandare da nufin bayar da ilimi kyauta ga yaran da suka rasa iyayensu a sakamakon ‘yan fashin daji, don hana dakile afkuwar rashin tsaro a nan gaba.

Sa’idu Dansadau ya tabbatar da cewa al’amuran tsaro sun inganta sosai a jihar biyo bayan rufe hanyoyin sadarwa.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: