Kungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta (IPMAN) ta yi barazanar dena kai man fetur zuwa jihohin Borno da Yobe

0 140

Kungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta (IPMAN) ta yi barazanar dena kai man fetur zuwa jihohin Borno da Yobe bisa zargin gwamnatin tarayya na gaza biyanta basussukan da ya kai naira biliyan 6.

Wannan dai na zuwa ne bayan shafe watanni 10 cikin rashin wutar lantarki a Maiduguri da kewaye sakamakon rikicin Boko Haram wanda ya yi illa ga harkokin zamantakewa da tattalin arziki a jihar.

A sanarwar da ta fitar kuma aka karanta a karshen taron masu ruwa da tsakin kungiyar a Maiduguri, Shugaban kungiyar na Jihar Borno, Alhaji Mohammed Kuluwu, ya ce kasa da kashi 10 na mambobinsu ne ke gudanar da ayyukansu saboda basukan.

Kuluwu ya yi nuni da cewa, kamata ya yi gwamnatin tarayya ta yi la’akari da ’yan kasuwan da suka fito daga jihohin biyu saboda irin rashin tsaro da suke fama da shi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: