Kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyatti Allah ta ce kimanin Mambobin ta dubu 10 ne aka kashe tare da raba miliyan 2 da muhallansu cikin shekaru 7 da suka gabata a Najeriya

0 61

Kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyatti Allah ta ce kimanin Mambobin ta dubu 10 ne aka kashe tare da raba Miliyan 2 da Muhallansu cikin shekaru 7 da suka gabata a kasar nan.

Kungiyar ta bayyana hakan ne a taron wata Mukala da ta shirya wanda aka gudanar a birnin tarayya Abuja, biyo bayan matsalolin tsaro da Fulani suke fuskanta.

Cikin wata sanarwa da ta fitar, Kungiyar ta ce daga shekarar 2015 zuwa yanzu, an raba Fulani da muhallansu, baya ga Dabbobi fiye da Miliyan 4 da aka kore ko kuma aka kashe.

Haka kuma ta ce Fulani ne suka fi fuskantar matsalolin hare-haren ramuwar gayya, da kashe musu Dabbobi da kuma garkuwa da su.

Kazalika ta bukaci a sake yin Nazari kan yadda harkokin Shari’a suke gudana, ta yadda za’a hukunta masu aikata laifi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: