Kungiyar Fulani ta caccakin Gwamnonin Arewacin Kasar nan da Sarakuna kan yadda suka yi watsi da Fulani

0 223

Kungiyar Fulani ta Miyatti Allah Kautal Hore, ta caccakin Gwamnonin Arewacin Kasar nan da kuma Sarakuna kan yadda suka yi watsi da Fulanin da suke zaune a Kudancin kasar nan.

Fulani na cigaba da fuskantar matsin Lamba daga kudancin Kasar nan, biyo bayan kakaba dokar kiwo a fili.

Da yake zantawa da manema labarai, Shugaban Kungiyar Miyatti Allah Kautal Hore na Jihar Bauchi Alhaji Muhammad Hussaini, ya ce akwai abin takaici kan yadda gwamnoni da kuma Sarakuna suka yi watsi da halin da Fulani suke ciki a kudancin kasar nan a taron da suka gudanar a Jihar Kaduna.

Alhaji Hussaini, ya koka kan yadda ake musgunawa Fulanin da suke kudancin kasar nan a lokacin da suke kiwon da dabbobin su.

Haka kuma ya ce dokar da ake neman a kakabawa Fulani ta hana Kiwo a sarari ta sabawa kundin tsarin mulkin kasa.

Kazalika, Shugaban Kungiyar ya kuma bayyana damuwarsa kan yadda gwamnonin suka fi mayar da hankali kan maganar Mulki da Siyasa fiye da kare rayuka da dukiyoyin yan Arewa a lokacin zaman.

Leave a Reply

%d bloggers like this: