Kungiyar Gwamnonin Jam’iyyar APC ta bayyana Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano a matsayin tauraro mai haske a siyasar Najeriya.

Kungiyar ta bayyana hakan ne a cikin sanarwar taya murnar da ta yi wa Ganduje yayin da ya cika shekaru 72 a duniya.

shugaban kungiyar gwamnoni kuma Gwamnan Jihar Kebbi, Atiku Bagudu ne ya bayyana hakan yayin zantawarsa da manema labarai a safiyar yau Asabar a Abuja babban birnin kasar.

Da yake jawabi, Bagudu ya ce Ganduje jagora ne na gari kuma mai hangen nesa da ya jajirce don tabbatar da hadin kan al’umma da kuma samar da Najeriya dunkulalliya.

Kazalika, Shugaban na kungiyar ya bayyana gwamna Ganduje a matsayin jagora na hakika la’akari da ayyukan da ya aiwatar domin ci gaban jam’iyyar APC.

Ya jaddada kudirin kungiyar wajen ganin ta aiwatar da shirye-shiryen da ta sanya a gaba na bunkasa jihohinsu ta hanyar samar da ayyukan yi, bunkasa tattalin arziki, dakile rashin daidaito da kuma rage talauci.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: