Kungiyar Hezbollah ta harba jirage marasa matuƙa cikin Isra’ila

0 206

Ƙungiyar Hezbollah mai ɗauke da makamai a Lebanon ta ƙadamar hare-haren rokoki fiye da 200 da jirage marasa matuƙa zuwa arewacin Isra’ila, a wani martani na kisan ɗaya daga cikin manyan kwamandojinta. Rundunar sojin Isra’ila ta ce an kashe sojanta guda a hare-haren, na Hezbollah. Sojojin na Isra’ila sun kuma ce sun mayar da martani kan mayaƙan ƙungiyar da sansanoninta da ke kudandin Lebanon. Kafofin yaɗa labaran Lebanon sun ce mutum guda ya mutu a wani harin jirgi maras matuƙi da Isra’ila ta kai garin Houla. Hare-haren na baya-bayan nan, sun kasance mafiya muni cikin watanni tara tsakanin kan iyakokin ƙasashen biyu. An kashe ɗaya daga cikin kwamandojin Hezbollaha wani hari ta sama da Isra’ila ta kai birnin Tyre na ƙasar Lebanon. Mohammed Nimah Nasser, ya kasance ɗaya daga cikin manyan jagororin ƙungiyar, kafin kisan nasa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: