Kungiyar Kare Hakkokin Tattalin Arziki ta baiwa shugaba Buhari wa’adin sa’o’i 72 da ya janye matakin toshe layukan wayar ‘yan Najeriya miliyan 72

0 37

Kungiyar Kare Hakkokin Tattalin Arziki, SERAP, ta baiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari wa’adin sa’o’i 72 da ya janye matakin toshe layukan wayar ‘yan Najeriya miliyan 72 da aka yi.

SERAP ta bukaci Buhari da ya umarci Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na zamani, Isa Pantami, da Hukumar Kula da Sadarwa ta Najeriya NCC da su gaggauta janye matakin da ya sabawa doka na hana sama da mutane miliyan 72 masu amfani da wayar tarho yin waya a layukansu.

A makon da ya gabata ne dai gwamnatin tarayya ta umarci kamfanonin sadarwa da su kulle duk layukan da ba su da alaka da su, saboda wa’adin tantancewar ya cika a ranar 31 ga Maris.

Biyo bayan umarnin, sama da masu rajista miliyan 72 an hana su yin kira.

Sai dai SERAP ta ce matakin na hana mutane yin waya tauye hakkin ‘yan Najeriya ne.

Leave a Reply

%d bloggers like this: