Kungiyar kwadago ta koka kan biyan mafi karancin albashi Naira dubu 35

0 162

Kungiyar kwadago ta masu masana’antu TUC, tayi kira ga gwamnatin tarayya ta kauda dukkan jinkirin da take yi wurin biyan mafi karancin albashi Naira dubu 35 a fadin kasar.

Shugaban kungiyar ta TUC Festus Osifo shine ya sanar da haka ga manema labarai, a karshen zaman majalisar zartarwa na Jiya a Abuja.

Idan za’a iya tunawa ranar 1 ga watan Oktoba shugaban kasa ya sanar za’a fara biyan ma’akatan naira dubu 35 na tsawon watanni 6 a matsayin tallafi sakamakon cire tallafin Man fetur.

Wannan wata yarjejeniya ce da aka cimma tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyoyin kwadago.

Festus Osifo yayi kira ga kamfanoni masu zaman kan su da su kara mafi karancin albashi na Naira dubu 35. Shugaban kungiyar ta TUC ya koka dangane da yadda mutane ke cikin wahala a fadin kasar nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: