Kungiyar lauyoyi masu kare marasa galihu a Najeriya ta ce Abduljabbar Nasiru Kabara bai cancanci samun kariyarsu ba, irin wadda suke bai wa masu karancin gata bayan ficewar lauyansa Ambali Muhammad daga shari’ar da ake yi masa ta yin batanci ga addini.

Wata kotun shari’ar musulunci da ke zamanta a kofar kudu ce ta nemi a bai wa Abduljabbar kariya daga kungiyar lauyoyin.

Tun daga watan Yunin bara ne yake fuskantar shari’ar yin batanci ga Annabi Muhammad (SAW) wanda gwanati Kano ta ce aikin nasa zai iya tunzura jama’a.

A jiya ne daraktan kungiyar Barista Mukhtar Labaran Usman ya shaida wa wata kotu cewa malamin bai cancanci a ba shi kariya ba saboda yana samun abin da ya wuce naira 30,000 wato mafi karancin albashida kasa ta yarda da shi.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: