Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU) ta sake tsawaita yajin aikin da take yi da wata uku

0 71

Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU) ta sake tsawaita yajin aikin da take yi da wata uku.

Hakan dai ya biyo bayan kammala taron Kwamitin Zartarwa na Kungiyar da ya gudana a Abuja a jiya Lahadi.

Shugaban Kungiyar Farfesa Emmanuel Osodeke, shine ya bayyana hakan, inda ya ce kungiyar ta bawa gwamnati ishashshen lokaci domin warware takaddamar da take tsakanin su.

’Yan sa’o’i dai kafin fara tattaunawar Kungiyar ASUU ta yi harsashen yiwuwar tsawaita yajin aikin saboda abin da ta kira halin-ko-in-kula daga bangaren gwamnati.

A ranar 24 ga watan Fabrerun 2022 ne Kungiyar ta shiga yajin aikin gargadi na makonni 4, domin biyan bukatun su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: