Kungiyar Malaman Larabci da Nazarin Addinin Musulunci Ta Kasa Tayi Allah Wadai Da Harin Da Aka Kai Masallacin Al-Aqsa
Kungiyar Malaman Larabci da Nazarin Addinin Musulunci ta kasa ta bukaci kungiyar Tarayyar Afirka (AU) da sauran kasashen duniya da su shiga tsakani domin dawo da zaman lafiya a Sudan.
Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar bayan taron kwamitin zartarwa na kungiyar da aka gudanar a jami’ar jihar Ekiti dake Ado-Ekiti.
Sanarwar na dauke da sa hannun Shugaban kungiyar Musa Adesina Abdu-Raheem da Sakatare Muhammad Shariff Ramadan.
Har ila yau, kungiyar ta yi Allah wadai da farmakin da jami’an tsaron yahudawan suka kai kan masallacin Al-Aqsa na kasar Falasdinu, inda suka hana al’ummar musulmin Palasdinawa amfani da masallacin musamman a watan Ramadan. Kungiyar ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya da ta tsawatarwa jami’an tsaron yahudawan da su shiga taitayinsu, sannan kasashen Larabawa su hada kai domin cimma manufa guda na tabbatar da zaman lafiya ga Palasdinawa.