Kungiyar Malaman manyan Makarantu (ASUU) reshen jihar Binuwai ta fara yajin aikin sai baba-ta-gani

0 61

Kungiyar Malaman manyan Makarantu a Jihar Binuwai ta fara yajin aikin sai baba-ta-gani.

‘yan jarida sun ruwaito cewa kungiyar ta kunshi kwalejojin ilimi da kuma kwalejin fasaha a jihar Benue.

Shugaban kungiyar da sakataren kungiyar, Dr Chagba Kurayemen da Dennis Eka, a wata sanarwa da suka rabawa manema labarai a Makurdi, sun bayyana cewa yajin aikin na daga cikin matakan da suka dauka na neman a biya mambobinsu hakkokinsu.

Kungiyar na nuna rashin amincewa da rashin biyan bashin watanni biyar na albashin 2017, da rashin aiwatar da shirin fansho na bayar da gudunmawar da bai dace ba; rashin aiwatar da sabon mafi karancin albashi wanda yakamata a fara a 2019.

A halin da ake ciki, taron da gwamnatin jihar ta yi da kungiyar malaman manyan makarantu a jihar Benue da aka gudanar a jiya ya kawo karshe cikin rashin jituwa.

Da aka tuntubi kwamishinan ilimi mai kula da harkokin ilimi, Godwin Oyiwona, a wani sako da ya aikewa manema labarai, ya ce an bukaci kungiyar ta dakatar da yajin aikin domin ba da damar tattaunawa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: