

- Mataimakin Gwamnan jihar Jigawa, Mallam Umar Namadi, shine ya lashe zaben fidda gwani na dan takarar gwamna a jam’iyyar APC - May 27, 2022
- Shugaba Buhari yace gwamnatinsa tana assasa ginshiki mai inganci na kyakykyawar rayuwa domin yara manyan gobe a Najeriya - May 27, 2022
- Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta haramta bangar siyasa da tare da yin amfani da duk wani makami ga yaran yan siyasa - May 27, 2022
Kungiyar Manoma ta Kasa reshen Jihar Jigawa ta ce matsalar karancin Man fetur a Kasa baki daya, zai shafi Noman Rani a Jigawa cikin wannan shekara.
Shugaban Kungiyar na Jihar Jigawa Alhaji Mai Unguwa Jaga, shine ya bayyana hakan a lokacin da yake tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN) a birnin Dutse.
Mai Unguwa Jaga, ya ce mafiya aka sarin Manoman Rani sun dogara ne da Injina domin yin bani a Gonakan su.
A cewarsa, Kungiyar zata yi zaman Jira na Makonni 3, domin ganin abinda Gwamnati zata yi domin saukaka wahalar da Man fetur din tare da saukaka farashin sa a Kasa baki daya.
Shugaban Kungiyar ya ce matukar gwamnati bata dauki matakai domin magance matsalar ba, farashin kayan abinci zai hauhawa, sakamakon Manoma da yawa masu baza sus amu damar noman ba.
Mai Unguwa Jaga, ya ce fada tsakanin Kasashen Ukraine da Russia, ya shafi farashin Alkama a kasashen Duniya.
A cewarsa, a yanzu haka ana sayar da buhun Alkama mai kwano 40 akan Naira dubu 33,000.
Haka kuma, ya ce Alkama, Masara da Albasa, na daga cikin abubuwan da Nomana suke yiwa bayi a shekarar nan.