Kungiyar marayu ta karamar hukumar Kaugama ta raba buhunan shinkafa da man girki da kuma kudi naira dubu biyu ga gidajen marayu 120

0 85

Kungiyar marayu ta karamar hukumar Kaugama ta raba buhunan shinkafa mai nauyin kilogram 25 da man girki da kuma kudi naira dubu biyu ga gidajen marayu 120 kowanensu a karamar hukumar Kaugama.

Shugaban kungiyar, Malam Ahmad Mai-unguwa ne ya bayyana haka lokacin kaddamar da rabon kayayyakin a fadar mai girma Hakimin Kaugama.

Malam Ahmad Mai-unguwa yayi bayanin cewa kungiyar ta kuma raba katon din taliya dai-dai da kudi naira dubu dai-dai ga gidajen masu karamin karfi guda 150 a yankin a matsayin tallafin watan Ramadan.

Yace kungiyar tana raba irin wadannan kayayyaki kowane watan Ramadan ga gidajen marayu da na masu karamin karfi domin tallafa musu a cikin wannan watan mai alfarma.

Leave a Reply

%d bloggers like this: