Kungiyar Masu Fafutikar Kafa Kasar Biafra ta ce bata da hannu kan kisan da ake yi a yankin Kudu Maso Gabas

0 59

Kungiyar Masu Fafutikar Kafa Kasar Biafra ta ce bata da hannu kan kisan da ake yi a yankin Kudu Maso Gabas.

Gwamnatin tarayya tayi zargin cewa yan kungiyar ta Biafra sun lalata ofisoshin yan Sanda 164 tare da kashe Jami’an tsaro 175 a yankin.

Da yake zantawa da manema Labarai a Abuja, Ministan Shari’a na Kasa Kuma Babban Lauyan Gwamnati Abubakar Malami SAN, ya ce yan Biafra sun kwace zanga-zangar EndSARS a shekarar 2020 wajen kaiwa hare-haren a ofisoshin Jami’an tsaro.

Amma da yake mayar da Jawabi, Kakakin Kungiyar ta Biafra Mista Emma Powerful, ya yi zargin cewa gwamnatin tarayya tana amfani da kafafen yada labarai wajen bata musu suna.

Da yake karyata kashe-kashen da ake cewa kungiyar Biafra ke yi, Kakakin Kungiyar ya ce kimanin Mambobin ta dubu 20,000 ne jami’an tsaro suka kashe.

Kazalika, ya ce Kungiyar Biafra bata neman tashin hankali sabanin yadda Babban Lauyan Gwamnati Abubakar Malami ya fada.

Leave a Reply

%d bloggers like this: