Kungiyar masu samar da pure water ta ce ta kara farashin ledar ruwan daga naira 150 zuwa 200 nan take sakamakon tashin farashin kayayyakin sarrafawa

0 64

Kungiyar masu samar da pure water ta ce ta kara farashin ledar ruwan daga naira 150 zuwa 200 nan take sakamakon tashin farashin kayayyakin sarrafawa.

Shugaban kungiyar na shiyyar Oye-Ekiti da Ikole-Ekiti, Tale Oguntoyinbo ne ya bayyana hakan a jiya a wata sanarwa.

Tale Oguntoyinbo ya ce karin farashin ya zama dole domin masu gidajen pure water su samar da ruwa mai inganci domin masu amfani da shi.

Shugaban ya bayyana cewa matakin kara farashin ba abu ne mai sauki ba, amma ya yi zargin cewa gwamnati ba ta yi wani abu ba wajen taimakawa masu samar da ruwa domin rage farashin kayayyakin.

Ya ce galibi a biranen da ake samar da leda da sauran kayayyakin samar da ruwan da kuma wutar lantarki, ana sayar da ledar ruwa tsakanin Naira 200 zuwa 250.

Ya kuma yi kira ga dimbin abokan huldar su da su yi hakuri dangane da matsalar tattalin arzikin da Nijeriya ke ciki a halin yanzu, tare da yin addu’ar samun sauki a gaba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: