Kungiyar Taliban ta nemi a ba ta damar ta gabatar da bayani a taron Majalissar Dinkin Duniya

0 67

Kungiyar Taliban ta nemi a ba ta damar ta yi wa shugabannin kasashen duniya jawabi a wajen babban taron Majalisar Dinkin Duniya da ake yi a wannan makon a birnin New York na kasar Amurka.

Wani kwamitin Majalisar Dinkin Duniyar zai yanke hukunci kan bukatar amma da wuya a amince a yanzu.

Taliban ta kuma zabi mai magana da yawunta da ke birnin Doha a kasar Qatar, Suhail Shaheen, a matsayin jakadan Afghanistan na Majalisar Dinkin Duniya.

Kungiyar, wacce ta kwace iko da Afghanistan a watan da ya gabata, ta ce jakadan tsohuwar gwamnatin da aka kifar a yanzu ba ya wakiltar kasar.

A cewar wani mai magana da yawun Majalisar Dinkin Duniya, wani kwamitin da ke duba cancanta ne ke duba bukatar da kungiyar ta nema ta yin jawabi a gaban shugabannin kasashen duniyar, wadanda mambobin kwamitin suka hada da Amurka da China da Rasha.

Leave a Reply

%d bloggers like this: