Kungiyoin NULGE, NUT, NUP, sun gabatar da shirin tantance adadin ma’aikata

0 98

Kungiyar Hadin Gwiwa ta Ma’aikatan Kananan Hukumomi, NULGE, da ta Malaman Makaranta, NUT, da ta Masu Karbar Fansho, NUP, sun gabatar da shirin tantance adadin ma’aikatan kananan hukumomi, malamai, da masu fansho a duk fadin kasar nan.

A karkashin Kwamitin Hadin Gwiwa na Ma’aikatan Kananan Hukumomi mai suna JAC, kungiyoyin sun bayar da shawarar dakatar da daukar ma’aikata na tsawon shekara daya daga lokacin da kotun koli ta yi hukunci kan biyan kudaden kananan hukumomi kai tsaye.

Haka kuma, sun bukaci sake fasalin hukumomin dake kula da ma’aikatan kananan hukumomi domin inganta aiki da ingantaccen tsarin kula da kudi. Sun kuma bukaci gwamnatin tarayya da ta samar da kayan aiki kamar motoci da kayan amfani a cibiyoyin koyar da sana’o’i, wanda kananan hukumomi zasu biya sannu a hankali.

Leave a Reply

%d bloggers like this: