Ya yinda kakar wasa ta shekarar 2024/2025 ke kawo ƙarshe a nahiyar Turai, tuni aka samu ƙungiyoyin da suka samu gurbi a gasar zakarun Turai ta kaka mai zuwa.
A bana ma ƙungiyoyi 36 ne za su fafata a gasar zakarun ta Turai, kuma tuni ƙungiyoyi 24 suka samu gurbin halartar gasar, sakamakon irin rawar ganin da suka taka a gasar lik ɗin ƙasashensu.
A gasar Firimiyar Ingila, ƙungiyoyi Liverpool da Arsenal ne kawai suka samu gurbi a babbar gasar ƙungiyoyin ta Turai a baɗi, sannan ana dakon ragowar ƙungiyoyi uku da za su mara musu baya.
A Italiya, an samu ƙungiyoyin Napoli da Inter Milan da Atalanta da kuma Juventus.
A Spain, zakarar gasar La liga Barcelona da Real Madrid da Atletico Madrid da Athletic Club da kuma Villarreal ne suka samu gurbin wakiltar ƙasar a gasar ta baɗi.
Ƙungiyoyin Bayern Munich da Borussia Dortmund da Bayer Leverkusen da kuma Frankfurt ne za su wakilci ƙungiyoin da ke fafatawa a gasar Bundesliga ta ƙasar Jamus, a gasar zakarun Turai.
A gasar Ligue 1 ta Faransa kuwa, ƙungiyoyin PSG da Marseille da kuma Monaco ne za su wakilci sauran, a gasar zakarun Turai.
Akwai ƙungiyoyin Ajex da PSV da za su wakilci ƙasar Netherlands, Sporting CP ta wakilci Portuugal, Union Saint-Gilloise ta wakilci Belguim, Galatasaray ta wakilci Turkiyya sai kuma Slavia Praha daga Jamhuriyar Czech.