Kungiyar tallafi mai fafutukar kare yara ta yi gargadin cewa kungoyoyin masu dauke da makamai sun mamaye asibitoci a kasar Sudan suna kwashe kayayyakin ceto rayuka.
Kungiyar tallafin tace tun a farkon wannan satin ne mayakan suka fatattaki wasu mutane 8 dake amfani da oxygen a wani asibiti dake Khartoum, babban birnin kasar.
Kungiyar tace an wawashe kayayyakin wasu kananan asibitoci guda 3 na ‘yan gudun hijira a yankin Darfur.
Majalisar dinkin duniya ta neman kimanin euro miliyan dubu 3 cikin gagggawa domin samun kudaden ayyukan jinkai a Sudan.
Majalisar ta dinkin duniya na hasashen cewa sama da mutane miliyan daya ne za su fice daga kasar kasancewar fada na cigaba da muni tsakanin sojoji da mayakan kungiyar RSF.
- Comments
- Facebook Comments