Kwamishinan ƴansandan jihar Sokoto ya tabbatar da mutuwar mutane 23 biyo bayan wani hari da aka kaiwa matafiya a jihar

0 164

Kwamishinan Yan Sandan Jihar Sokoto CP Kamaludeen Okunola, ya tabbatar da mutuwar mutane 23 biyo bayan wani hari da aka kaiwa Matafiya a yankin Angwan Bawa, take Karamar Hukumar Sabon Birni ta Jihar.

Kwamishinan ya tabbatar da hakan ne jin kadan bayan ganawa da Gwamnan Jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal, a wani taron Majalisar tsaro wanda Gwamnan ya jagoranta a yau.

CP Kamaludeen Okunola, ya bayyana kashe Matafiyan a matsayin abin takaici, inda ya kara da cewa tuni aka tura da karin Jami’an tsaro zuwa wurin da lamarin ya faru domin dawo da zaman lafiya tare da kama wadanda suka aikata laifin.

Tun da farko, Kakakin rundunar Yan sandan Jihar Sokoto Sanusi Abubakar, ya bayyana cewa Motar na dauke da Fasinjoji 24 ne a lokacin da yan bindigar suka kai musu hari, lamarin ya yi sanadiyar mutuwar mutane 18.

Sai dai daga baya ya bayyana cewa mutane 9 sun kubuta daga cikin matafiyan, inda kuma 21 suka kone kurmus.

Leave a Reply

%d bloggers like this: