Labarai

Kwamishinan Yaki da Talauci ta Jihar Borno ajiye mukamin sa domin tsayawa takarar dan majalisar Dokokin Jihar mai wakiltar Mazabar Chibok

Kwamishinan Yaki da Talauci ta Jihar Borno Hon Nuhu Clark, ya ajiye mukamin sa domin tsayawa takarar dan majalisar Dokokin Jihar mai wakiltar Mazabar Chibok karkashin tutar Jam’iyar APC.

Mista Clark, ya fadawa Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa NAN a Maiduguri cewa ya ajiye Mukamin ne domin tsayawa takarar dan Majalisar Jiha mai wakiltar Chibok.

Kwamishinan ya ce an zabe shi a matsayin shugaban karamar hukumar Chibok a shekarar 1999, inda ya samarwa mutanen yankin abubuwan more rayuwa wanda suke rayuwa har yanzu da shi.

Hon Nuhu Clark ya godewa Gwamna Babagana Zulum bisa bashi dama domin ya yi aiki tare da shi, inda ya ce kasancewar sa tsohon shugaban karamar hukuma, kuma shugaban Matasa na Jihar kuma tsohon mai bawa gwamnan Jihar shawara ya na da gogewar aiki idan aka zabe shi kujerar dan Majalisa.

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa NAN, ya rawaito cewa Kwamishinan Albarkatun Noma na Jihar Bukar Talba, ya yi murabus domin tsayawa takarar dan majalisar tarayya mai wakiltar Nganzai/Monguno/ Marte karkashin tutar Jam’iyar APC.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: