Labarai

Kwamishinan Yan Sandan Jihar Kaduna ya bawa matafiyan da suke bin hanyar Kaduna zuwa Abuja tabbacin cewa an samu tsaro mai inganci a hanyar

Kwamishinan Yan Sandan Jihar Kaduna Mista Yekini Ayoku, ya bawa matafiyan da suke bin hanyar Kaduna zuwa Abuja tabbacin cewa an samu tsaro mai inganci a hanyar.

Kakakin Rundunar Yan sandan Jihar ASP Muhammed Jalige, shine ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai, inda ya ce Kwamashinan ya bada tabbacin ne a lokacin da ya kai ziyara babbar hanyar.

ASP Jalige ya ce kwamishinan ya samu rakiyar manyan yan sanda daga rundunar, inda kuma kwamishinan ya gana da Jami’an tsaron da suke aiki a shingayen da suke hanyar.

Kwamishinan ya yabawa Jami’an tsaron inda ya basu tabbacin cewa rundunar zata kula da walwalar su.

Kazalika, ya shawarci al’umma su kai rahotan zirga-zirgar mutanen da basu yarda da suba, ga Jami’an tsaro.

NAN

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: