Kwamitin kananan hukumomi na majalisar dokokin jihar Jigawa ya fara duba yadda ake gudanar da ayyuka a faɗin jihar
Kwamitin kula da harkokin kananan hukumomi na majalisar dokokin jihar Jigawa ya fara rangadin duba yadda ake gudanar da ayyukan kananan hukumomi a faɗin jihar, domin tabbatar da adalci da gaskiya wajen amfani da kuɗaɗen jama’a.
Shugaban kwamitin, Aminu Zakari, ne ya bayyana haka yayin wata ziyarar kwana biyu da suka kai karamar hukumar Buji a ranar Talata, inda suka duba yadda ake aiwatar da kasafin kuɗi da kuma tabbatar da ingantaccen amfani da dukiyar gwamnati.
Ya ce wannan ziyara na daga cikin manyan ayyukan kwamitin na sa ido, kuma za su kai irin wannan ziyara zuwa dukkan kananan hukumomi 27 da ke cikin jihar domin ganin an gudanar da mulki bisa tanadi na doka.
A nasa bangaren, shugaban karamar hukumar Buji, Najib Gantsa, ya nuna farin ciki da ziyarar, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen samun shawarwari da jagoranci don kyautata harkokin gudanarwa a matakin ƙananan hukumomi.