- Mataimakin Gwamnan jihar Jigawa, Mallam Umar Namadi, shine ya lashe zaben fidda gwani na dan takarar gwamna a jam’iyyar APC - May 27, 2022
- Shugaba Buhari yace gwamnatinsa tana assasa ginshiki mai inganci na kyakykyawar rayuwa domin yara manyan gobe a Najeriya - May 27, 2022
- Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta haramta bangar siyasa da tare da yin amfani da duk wani makami ga yaran yan siyasa - May 27, 2022
Kwamitin kare hakkin mai saye da sayarwa na jihar Jigawa ya samu nasarar kama wani mai suna Jamilu Abdullahi a kofar babban asibitin Jahun bisa laifin yin algus a manja.
Shugaban Hukumar, Mallam Farouk Abdallah, ya sanar da hakan a wata sanarwa inda yace an samu mutumin ne da laifin hada koko da manja a garin Jahun.
Yace tuni kotun tafi da gidanka ta kwamitin ta zartar masa da hukuncin daurin watanni 6 a gidan gyaran tarbiyya ko kuma zabin biyan tarar naira dubu 60.
Ya kara da cewa kotun ta bashi wa’adin kwanaki 30 domin daukaka kara.
Farouk Abdallah ya kara da cewar tuni kotun ta kwace manjan tare da gargadin cewar muddin ya sake aikata irin wannan laifi zai tafi gidan maza na watanni 3 kafin fara sabuwar sharia.
Ya kuma ce hukuncin zai kasance izna ga masu yin algus a kayayyakin abinchi.