Kwamitin kare hakkin mai saye da sayarwa na jihar Jigawa ya samu nasarar kama wasu mutane hudu a kasuwar Hadejia bisa laifin cakuda kasa da ruwa a bahu 37 na kanwa.

Shugaban kwamitin Alhaji Farouk Abdallah Mallam Madori ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai.

Yace an samu mutanen ne da laifin cakuda kasa da ruwa da garin kanwa suna shanyawa sannan in ya bushe su zuba a buhu su kai kasuwa.

Alhaji Farouk Abdallah ya ce tuni suka mika su gaban kotun tafi da gidanka domin su girbi abin da suka shuka.

Kotun ta aike su zuwa gidan gyaran tarbiyya na mako guda, bayan sun yi sati guda an dawo dasu kotun ta daure su na tsawon watanni goma goma ko zabin biyan tarar kudi naira dubu tamanin kowannensu tare da kwace buhunan kanwar gaba daya.

Mutanen sun hadar da Kawu Muhammad da Babangida Muhammad da Usman Muhammad da Danladi Mai Kanwa.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: