Kwamitin kare hakkin mai saye da sayarwa na jihar Jigawa ya samu nasarar kama wani mai suna Muhammad Abdullahi dake garin Dan-ama a karamar hukumar Gumel bisa lefin yin cakuda ridi da kasa.

Shugaban kwamitin Mallam Farouk Abdallah ya bayyana bayyana hakan a wata sanarwa da ya aiko dakinmu na labarai.

Yace sun mika mutumin ga kotun tafi da gidanka wadda ta zartar masa da hukuncin wata hudu a gidan gyaran tarbiyya ko kuma biyan tarar naira dubu 50.

Kotun ta ce zata masa daurin talala da zarar an sake kama shi da aikata irin wannan lefi na tsawon watanni uku kafin ayi masa sabuwar sharia.

Mallam Farouk Abdallah yace hukuncin zai kasance Izna ga masu aikata algus a kayayyakin amfanin gona.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: