Kwamitin rikon kwarya na Jam’iyyar APC ya ce tarukan jam’iyyar da aka shirya gudanarwa yananan a ranar Asabar

0 72

A halin da ake ciki, kwamitin rikon kwarya na Jam’iyyar APC ya ce tarukan jam’iyyar da aka shirya gudanarwa a ranar Asabar, zai gudana kamar yadda aka tsara.

Ana bayyana damuwa game da tarukan bayan hukuncin Kotun Koli kan zaben Gwamnan jihar Ondo.

Bayan yanke hukuncin, karamin Ministan Neja Delta, Festus Keyamo, ya shawarci APC da ta dakatar da duk wasu shirye-shiryen gudanar da tarukan.

Amma a wata sanarwa a yau, sakataren kwamitin rikon jam’iyyar, John Akpan, ya ce hukuncin Kotun Koli ba shi da wata alaka da tarukan.

Kotun kolin ta yi watsi da daukaka karar da dan takarar jam’iyyar PDP, Eyitayo Jedege, ya shigar.

Amma mai shari’a Mary Odili, a nata hukuncin marar rinjaye, ta goyi bayan bukatar Jegede na cewa takardar tsayar da Akeredolu takara, wanda Gwamna Mai Mala Buni na Jihar Yobe ya sanya hannu, ba ta da inganci a karkashin Sashe na 183 na kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999.

Leave a Reply

%d bloggers like this: